Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila.
Ko ma yayinda mutanen nan suke yi wa Ubangiji sujada, ba su daina bauta wa gumakansu ba. Har yă zuwa yau, ’ya’yansu da jikokinsu sun ci gaba da bin gurbin kakanninsu.