2 Sarakuna 17:20 - Sabon Rai Don Kowa 202020 Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki20 Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra'ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.