2 Sarakuna 12:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Sa'an nan Yehoyada, firist, ya ɗauki akwati, ya huda rami a murfin, sa'an nan ya ajiye shi kusa da bagade a sashin dama na shiga Haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka saka dukan kuɗin da aka kawo a Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.