2 Sarakuna 12:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.