Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.
A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.
Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba.