2 Sarakuna 11:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Amma Yehosheba 'yar sarki Yoram, 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda aka kashe, ta ɓoye shi da mai renonsa, an yi ta renonsa cikin ɗaki. Da haka ta tserar da shi daga Ataliya, har ba a kashe shi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.