2 Sarakuna 11:19 - Sabon Rai Don Kowa 202019 Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki19 ya kuma sa shugabanni, da Keretiyawa, da matsara, da dukan jama'ar ƙasar, su fito da sarki daga Haikalin Ubangiji, suka rufa masa baya ta ƙofar matsara zuwa gidan sarki. Suka sa shi a gadon sarautar sarakuna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada.