2 Sarakuna 11:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Yehoyada kuwa ya yi alkawari tsakanin Ubangiji, da sarki, da jama'a, yadda za su zama jama'ar Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da jama'a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.