2 Sarakuna 11:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Da ta duba, sai ta ga sarki a tsaye kusa da ginshiƙi bisa ga al'ada, shugabanni da masu busa kuwa suna tsaye kusa da sarki. Dukan mutanen ƙasar suna ta murna suna ta busa ƙaho. Sai Ataliya ta kece tufafinta, ta yi ihu, tana cewa, “Tawaye, tawaye!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.
Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.