2 Sarakuna 10:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Da safe, sa'ad da ya fita, ya tsaya, sai ya ce wa mutane duka, “Ba ku da laifi, ni ne na tayar wa maigidana har na kashe shi, amma wane ne ya kashe dukan waɗannan? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”