2 Sarakuna 1:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Ahaziya fa ya fāɗo daga tagar ɗakin samansa a Samariya ya ji rauni. Saboda haka ya aiki masinjoji, yana cewa, “Ku je ku tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron, ku ga ko zan warke daga wannan rauni.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.