2 Samaʼila 8:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan kayayyaki wa Ubangiji, yadda ya yi da zinariya, da kuma azurfa daga dukan al’umman da ya mallaka, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al'umman da ya mallaka, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.