2 Samaʼila 7:27 - Sabon Rai Don Kowa 202027 “Ya Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka bayyana wa bawanka cewa, ‘Zan gina maka gida.’ Saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali yă miƙa maka wannan addu’a. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki27 Gama kai, ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kai ne ka sanar wa ni bawanka, cewa, za ka sa gidana ya kahu, saboda haka ni bawanka na sami ƙarfin halin yin wannan addu'a a gare ka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”
In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.