2 Samaʼila 7:23 - Sabon Rai Don Kowa 202023 Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki23 Ba wata al'umma kuma a duniya wadda take kama da jama'arka Isra'ila, wadda kai Allah ka fansa ta zama jama'arka. Ka mai da kanka sananne. Ka yi wa jama'arka manyan abubuwa masu banmamaki. Ka kori al'ummai da gumakansu a gaban jama'arka, waɗanda ka fansa daga Masar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |