2 Samaʼila 7:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 yadda suka yi tun lokacin da na naɗa shugabanni bisan mutanena Isra’ila, zan kuma hutashe ka daga hannun abokan gābanka. “ ‘Ubangiji ya furta maka cewa Ubangiji kansa zai kafa maka gida. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.