Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.
Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.
Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.