2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina; maganarsa tana a harshena.
2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina, Saƙonsa yana kan leɓunana.
Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.
Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,
Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’
Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka.