Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa.
Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.”