20 Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne, Asahel?” Ya ce, “Ni ne.”
20 Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?” Ya amsa, “Ni ne.”
Ya fafari Abner, bai juya dama ko hagu ba, yayinda yake fafararsa.
Sai Abner ya ce masa, “Yi dama ko hagu ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka ƙwace makamansa.” Amma Asahel bai bar fafararsa ba.