2 Samaʼila 19:42 - Sabon Rai Don Kowa 202042 Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki42 Dukan mutanen Yahuza suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, “Domin sarki ɗan'uwanmu ne na kusa. Me ya sa kuke fushi a kan wannan al'amari? Me muka ci a jikin sarki, ko kun ji ya ba mu wani abu ne?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.