2 Samaʼila 18:32 - Sabon Rai Don Kowa 202032 Sarki ya ce wa mutumin Kush, “Saurayin nan Absalom, yana nan lafiya?” Mutumin Kush ya ce, “Allah yă sa abokan gāban ranka yă daɗe, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki32 Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?” Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!