2 Samaʼila 17:25 - Sabon Rai Don Kowa 202025 Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki25 Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.