To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’