Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 12:24 - Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

24 Sa'an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta'aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 12:24
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.


Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne.


kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa ’yar Ammiyel ta haifa.


Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.


kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya.


amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba.


Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba?


Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.


Game da Benyamin ya ce, “Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi, gama yana tsare shi dukan yini, wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa.”


Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,


Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ