Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 12:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sa’an nan Dawuda ya tashi daga ƙasa. Bayan ya yi wanka, ya shafa mai, ya kuma canja rigunarsa, sa’an nan ya shiga gidan Ubangiji ya yi sujada. Sai ya tafi gidansa, ya nemi a ba shi abinci, aka ba shi, ya kuwa ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa'an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 12:20
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada


Ki yi wanka ki fesa turare, ki kuma sa tufafinki mafi kyau. Sa’an nan ki gangara zuwa masussuka, amma kada ki bari yă san cewa kina a can sai ya gama ci da sha.


Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka,


Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum,


Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.


Sa’an nan Sarki Dawuda ya je ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ko gidana, har da ka ɗaga mu zuwa wannan matsayi?


Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan.


Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji.


Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.


Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?” Suka ce, “I, ya rasu.”


Barorinsa suka ce masa, “Me ya sa kake yin haka? Yayinda yaron yake da rai, ka yi azumi, ka kuma yi kuka, amma yanzu da yaron ya mutu, ka tashi, ka kuma ci abinci!”


Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu.


Mefiboshet, jikan Shawulu, shi ma ya gangara don yă taryi sarki. Tun daga ranar da sarki ya gudu har ran da ya komo lafiya, Mefiboshet bai lura da ƙafafunsa, ko yă aske gemunsa, ko yă wanke tufafinsa ba.


Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;


Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.


Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.


Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.


Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.”


Saboda haka sai Sama’ila ya koma tare da Shawulu, Shawulu kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ