13 A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
13 Ina roƙonku kamar 'ya'yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci.
’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.
Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa,
Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.
Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.
Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka ’yantar da zuciyata.