Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.
“Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”
Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.