Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba ni da abin jin kunya a ciki.
Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.