Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.
Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba.
Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne.