Don haka ina farin ciki in kashe dukan abin da nake da shi a kanku, har in ba da kaina ma dominku. In na ƙaunace ku fiye da haka, za ku rage ƙaunarku gare ni ne?
Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa.
Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
“Maɗaukaki, Allah, Ubangiji! Maɗaukaki, Allah, Ubangiji ya sani! In mun yi wannan cikin tawaye ko rashin biyayya ga Ubangiji ne, kada ku bar mu da rai yau.
Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.