Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.
Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.
Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.
Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kāsa waɗannan mafiffitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.
Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!
Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku!
Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”
A daidai sa’ad da Bulus yana shirin yin magana, sai Galliyo ya ce wa Yahudawan, “Da a ce ku Yahudawa kuna gunaguni game da munafunci, ko kuma wani babban laifi, da sai in iya sauraronku.
Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”
Yoshuwa kuma ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, me ya sa ka sa mutanen nan suka ƙetare Urdun don ka bari mu shiga hannun Amoriyawa su hallaka mu? Kila da mun haƙura mun zauna a ɗaya gefen Urdun da ya fi mana!