2 Bitrus 2:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.