Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke.
Ba nuna muku iko a kan bangaskiyarku muke yi ba, sai dai muna aiki tare da ku ne saboda farin cikinku, domin bisa ga bangaskiya ce kuke tsaye da ƙarfi.
Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu.
Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.