Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba.
Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,