Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’
Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a.
“Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
Dattijon nan, Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya.