A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.
Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.
A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau.