Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 2:17 - Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Amma, ’yan’uwa, sa’ad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci (a jiki, ba a tunani ba), daga cikin marmarinmu mai tsanani mun yi duk abin da muke iya yi mu gan ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

17 Ya ku 'yan'uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 2:17
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.


Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku.


Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.


Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.


Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku,


Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala.


Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.


Da dare ya yi, sai ’yan’uwa suka sallami Bulus da Sila su tafi Bereya. Da suka isa can, sai suka shiga majami’ar Yahudawa.


Amma Elisha ya ce masa, “Ashe, ba ina tare da kai a ruhu ba sa’ad da mutumin ya sauko daga keken yaƙinsa ya tarye ka. Kana gani wannan lokaci ne da za a karɓi kuɗi, da riguna, da gonar inabi, da tumaki, da bijimai, da bayi maza da mata?


Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.


Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”


Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”


Yanzu ka gudu domin kana marmari komawa gidan mahaifinka. Amma don me ka sace mini gumakana?”


Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ