5 Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da ’ya’yansa maza.
da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela.
Zuriyar Yahuda bisa ga kabilansu, daga Shela, kabilar Shelayawa daga Ferez, kabilar Ferezawa; daga Zera, kabilar Zerawa;
Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690.