(Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)
Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)
Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”