Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.
Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan;