1 Tarihi 5:26 - Sabon Rai Don Kowa 202026 Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki26 Don haka Allah na Isra'ila ya zuga Ful, Sarkin Assuriya, wato Tiglat-filesar, ya zo ya kwashe su, ya kai su bauta, wato su Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa. Ya kai su Hala, da Habor, da Hara, har zuwa kogin Gozan, can suke har yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.