Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin ce; ita daga Urushalima ne.
Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.
Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok.
Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.