Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.
Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.