1 Tarihi 27:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila, bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16-22 Ga jerin sunayen masu mulkin kabilan Isra'ila. Ra'ubainu: Eliyezer ɗan Zikri, Saminu: Shefatiya ɗan Ma'aka, Lawi: Hashabiya ɗan Kemuwel, Haruna: Zadok, Yahuza: Eliyab ɗaya daga cikin 'yan'uwan sarki Dawuda, Issaka: Omri ɗan Maikel, Zabaluna: Ishmaiya ɗan Obadiya, Naftali: Yerimot ɗan Azriyel, Ifraimu: Hosheya ɗan Azaziya, Manassa ta Yamma: Yowel ɗan Fedaiya, Manassa ta Gabas: Iddo ɗan Zakariya, Biliyaminu: Yawasiyel ɗan Abner, Dan: Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabannin kabilai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.