1 Tarihi 27:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki1 Ga lissafin kawunan iyalin Isra'ilawa, da shugabannin dangi, da jama'a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.