Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 26:31 - Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

31 Yeriya shi ne shugaban zuriyar Hebron bisa ga asalinsu. A shekara ta arba'in ta sarautar Dawuda, sai aka bincika, aka tarar akwai ƙarfafan mutane, jarumawa a cikinsu, a Yazar ta Gileyad.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 26:31
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.


Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.


Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.


Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima.


Ya yi sarauta shekaru arba’in a bisa Isra’ila. Wato, shekaru bakwai a Hebron da kuma talatin da uku a Urushalima.


Yankin ƙasarsu ya ƙunshi Yazer, da dukan garuruwan Gileyad, da rabin ƙasar Ammonawa har zuwa Arower kusa da Rabba,


Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ