22 Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
22 Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.
Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
Kabilar Kohat su ne, Amramawa da Izharawa da Hebronawa da Uzziyelawa; waɗannan su ne kabilar Kohatawa.
Sunayen mutanen Kohat kuwa su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
’Ya’yan Izhar maza, su ne, Kora, Nefeg da Zikri.
Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.