Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 23:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

4 Sai Dawuda ya ce dubu ashirin da dubu huɗu (24,000) daga cikinsu za su yi hidimar Haikalin Ubangiji, dubu shida (6,000) kuma su zama manyan ma'aikata da alƙalai,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 23:4
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.


Ku naɗa alƙalai da shugabanni don kowace kabila, a kowane birnin da Ubangiji Allahnku yake ba ku, za su kuma shari’anta mutane ba nuna bambanci.


Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.


“Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.


Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.


Yowel ɗan Zikri ne babban shugabansu, Yahuda kuma ɗan Hassenuwa, ya shugabanci Yanki na Biyu na birni.


Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.


“ ‘A duk wani rashin jituwa, firistoci za su zama alƙalai su kuma yanke magana bisa ga farillaina. Za su kiyaye dokokina da ƙa’idodina a dukan ƙayyadaddun bukukkuwana, su kuma kiyaye Asabbataina da tsarki.


Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.


sun lura da ma’aikata, suka kuma lura da dukan masu aiki daga aiki zuwa aiki. Waɗansu Lawiyawan su ne marubuta, magatakarda da kuma masu tsaron ƙofofi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ