1 Tarihi 22:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 Dawuda ya ce, “Ɗana Solomon matashi ne kuma bai gogu ba, kuma gidan da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, sananne da kuma mai daraja a idon dukan al’ummai. Saboda haka zan yi shirye-shirye saboda shi.” Sai Dawuda ya yi ɗumbun shirye-shirye kafin mutuwarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 Dawuda kuwa ya ce, “Ɗana Sulemanu yaro ne, bai gogu da duniya ba. Ga shi, Haikalin da za a gina wa Ubangiji zai zama mai ƙayatarwa ƙwarai, zai zama sananne mai daraja cikin dukan ƙasashe, saboda haka sai in tanada masa.” Domin haka Dawuda ya tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa kafin rasuwarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Yanzu ina shirin ginin haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, in kuma keɓe shi gare shi don ƙona turare mai ƙanshi a gabansa, don kuma ajiyar burodi mai tsarki kullum, da kuma don miƙa hadayun ƙonawa kowace safiya, kowace yamma, da a Asabbatai da Sababbin Wata, da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwan Ubangiji Allahnmu. Wannan dawwammamiyar farilla ce don Isra’ila.