1 Tarihi 22:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 “Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.